Connect with us

News

Gwamnatin Tarraya Ta Biya Billiyan 169.4 Amatsayin Tallafin Man Fetur A Watan Agusta 2023

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Alamu sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta biya Naira biliyan 169.4 amatsayin tallafi a watan Agusta domin cigaba da samun farashin man Fetur akan Naira 620 kowace lita.

Wannan na zuwa ne duk da irin tabbacin da shugaba Bola Tinubu ya sha bayarwa cewa tallafin mai ya tafi kenan.

An Kama Wata Mata Da Muggan Kwayoyi A Filin Jirgin Sama Na Malam Aminu Kano

Wani kundi na kwamitin kasafta arzikin kasa wanda jaridar dailytrust ta gani, ya nuna cewa a cikin watan Agustan 2023, Kamfanin gasa na kasa NLNG ya biya dala milliyan 275 amatsayin ribar kamfanin NNPC Limited.

Bayan haka, kamfanin NNPC Limited ya yi amfani da dala miliyan 220 kwatankwacin Naira billiyan 169.4 daga cikin dala miliyan 275 wajen biyan tallafin man fetur, inda aka yi zargin cewa ya rike dala miliyan 55 ba bisa ka’ida ba.

Advertisement

Wannan dai ya karfafa ikirari da shugaban PENGASSAN na kasa, Festus Osifo ya yi cewa saboda tsadar danyen mai a kasuwannin duniya da kuma karuwar farashin canji, har yanzu gwamnati na biyan tallafin man fetur.

A wani labarin kuma An Kama Wata Mata Da Muggan Kwayoyi A Filin Jirgin Sama Na Malam Aminu Kano

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending