Connect with us

News

kashi 80 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar mashako ba su yi allurar rigakafi ba -Dr Faisal Shu’aibu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce kaso 97 cikin 100 na mutanen da suka kamu da cutar mashako da akafisani da Diphtheria a Najeriya sun fito ne daga jihohi biyar na arewa.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko na  kasa, Dr Faisal Shuaib ne bayyana haka a wata ziyarar aiki domin duba matakan da ake dauka na yaki da barkewar cutar mashako a jihar Kano, ya ce jihohin su ne Kano da Yobe da Borno da Katsina da kuma Kaduna.

Advertisement

Tinubu Ya Amince Da Amfani Da Kankare Wajen Yin Tituna – Ministan Ayyuka 

Dr Faisal wanda ya ziyarci cibiyar kula da masu fama da cutar mashako dake asibitin kwrarru na Murtala Muhammed a Kano, ya ce bayanai sun nuna sama da kashi 80 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar da kuma wadanda suka mutu ba su yi allurar rigakafi ba. .

 

Advertisement

Ya kara da cewa Najeriya na bukatar samun tsarin rigakafi na yau da kullum mai inganci kuma akwai bukatar iyaye su kai rahoton duk wata daga ta cutar daga ‘ya ‘yansu zuwa kwararru domin daukar matakai.

 

Advertisement

Ya yi tsokaci kai tsaye kan labaran karya da game da alluran rigakafi, kamar yadda aka yada jita-jita akan cewa rigakafin polio yana haifar da rashin haihuwa.

 

Advertisement

Daga nan, Dokta Faisal Shuaibu ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai da kafafen yada labarai domin yada sahihan bayanai dangane da rigakafi

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending