Connect with us

News

Rundunar sojin sama Sun Halaka Mayakan ISWAP Kimanin 100

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Rundunar sojin saman kasar nan ta baiyana cewar dakarunta masu gudanar da shirin sumame na Hadin Kai da Hadarin Daji sun samu nasarar halaka mayakan ISWAP da sauran mayakan tada kayar baya kimanin 100, a luguden wuta ta sama da ta yi masu.

Gwamnatin jihar Kano za ta samar da kyakkyawan yanayi ga sabon shirin SFH

Wata sanarwa da kakakin rundunar Edward Gabkwet ya fitar, Ya ce da safiyar ranar Asabar din data gabata, Dakarun suka farwa sabbin maboyar ‘yan tada kayar bayan dake Bukar Merama kusa da tabkin Chadi a jihar Borno.

Ya kara da cewar Luguden wutar ta sama ya zama wajibi biyo bayan yadda yan tada kayar bayan suka mayar da yankunan Suwa zuwa Bukar Meram, maboyarsu da suke shirya kai hare-hare.

A wani labarin kuma Gwamnatin jihar Kano za ta samar da kyakkyawan yanayi ga sabon shirin SFH

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending