News
Gwamnan Jihar Legas ya sake buɗe kasuwar Mile 12 kwana biyu bayan rufe ta
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bada umarnin gaggawa kan sake buɗe fitacciyar kasuwar nan ta Mile 12 biyo bayan gamsuwa da matakan tsaftace muhalli da aka ɗauka a kasuwar.
A ranar Juma’ar da ta gabata gwamnatin jihar ta rufe kasuwar Mile 12 tare da kasuwar Owode Onirin saboda dalilai masu nasaba da rashin tsaftace muhalli.
Sanata Elisha Abbo Ya Ce Shugaban Majalisar Dattawa Ne Yasa Kotu Ta Sauke Shi Daga Kan Kujerarsa
Sanarwar da gwamnatin ta fitar a ranar Litinin ta bakin Kwamishinan Muhalli da Ruwa na jihar, Mr Tokunbo Wahab, ta ce an sake buɗe kasuwar ce bayan gamsuwa da matakan tsaftace muhallin da aka ɗauka a kasuwar
Kwsmishinan ya ce gwamnatin jihar ba ta ɗaga ƙafa kan batutuwan da suka shafi tsaftar muhalli da lafiyar al’umma, don haka ya ce gwamnatin ba za ta ɓata lokaci ba wajen ɗaukar matakin da ya dace a duk inda aka saɓa wannan tsari.
“Ba zai yiwu mu ci gaba da zama masu nuna halin ko-in-kula ba dangane da muhalli. Dole ne mu daina nuna rashin kulawa ga muhallinmu, in ji shi.
