Connect with us

News

Sanata Elisha Abbo Ya Ce Shugaban Majalisar Dattawa Ne Yasa Kotu Ta Sauke Shi Daga Kan Kujerarsa

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Sanatan Adamawa ta Arewa da kotu ta sauke shi daga kan kujerarsa, Elisha Abbo, Ya zargi shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio da zama kanwa uwar gami a hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, na sauke shi daga kan kujerarsa.

jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa A jiya ne kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta soke zaben da aka yiwa Sanata Elisha Abbo na jam’iyyar APC, ta re da aiyana dan takarar jam’iyyar PDP Amos Yohanna a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben kujerar sanatan.

Advertisement

Kotu Ta  Yankewa Wani Mai Safarar Miyagun Kwayoyi A Nan Kano Daurin Shekara 10

A martanin da ya mayar kan hukuncin da kotun ta yanke, Sanata Elisha Abbo ya zargi shugaban majalisar dattawa Sanata Akpabio da yin uwa da makarbiya wajen ganin kotun ta yanke hukuncin, Ya kuma ce akwai ragowar wasu sanatoci guda hudu da basu zabi Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa ba, da suma kotun zata sauke su daga kan kujerunsu.

Ya kara da cewar sanata Orji Uzor Kalu na jam’iyyar APC mai wakiltar Abia ta arewa, shin kan sahun gaba da kotu zata sauke daga kan kujerarsa.

Advertisement

 

Sai dai ya bukaci magoya bayansa dasu kwantar da hankalinsu, tare da cin alwashin sake neman kujerar sanatan a shekarar 2027.

Advertisement

Sai dai a martanin da shugaban majalisar dattawan ya mayar, ya musanta cewar yana da hannu a hukuncin da aka yanke, inda ya baiyana cewar babu wani dalili da zai sa shi ya rika yiwa abokan aikinsa wani bita da kulli.

A wani labarin kuma Kotu Ta  Yankewa Wani Mai Safarar Miyagun Kwayoyi A Nan Kano Daurin Shekara 10

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending