News
Kotu Ta Yankewa Wani Mai Safarar Miyagun Kwayoyi A Nan Kano Daurin Shekara 10
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a nan Kano karkashin mai shari’a S.A Amobeda ta yankewa wani kasurgumin mai safarar miyagun kwayoyi mai suna Muhammad Sambo daurin shekara 10 a gidan gyaran hali.
Sambo na daga cikin masu safarar miyagun kwayoyi da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kano ta kama a cikin watan Octoban da muke ciki.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sadiq Maigatari ya fiyar a ranar Litinin, ta ce bayan gurfanar da wanda ake tuhumar gaban kotun, an yanke masa hukuncin daurin shekara 10.
Sanarwar ta baiyana cewar kwamandan hukumar Abubakar Ahmad ne ya jagoranci gurfanar da wanda aka yanke hukuncin gaban kotu.
A wani labarin kuma Kungiyar SERAP Ta Kai Karar Majalisar Dokoki Ta Kasa Saboda Siyawa Kowane Dan Majalisar Motar Milyan 130
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
