Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Sako Malamar Jam’iar Nasarawa Da Suka Sace

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

An sako Malamar Jami’ar Jihar Nasarawa, Dakta Comfort Adokwe, wadda aka yi garkuwa da ita ranar Lahadi.

Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa, a daren Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da Adokwe, malama a tsangayar gudanarwa na jami’ar, kuma mataimakiyar darakta a fannin nazarin jinsi na makarantar, daga gidanta da ke Angwan Jaba a garin Keffi.

Hukumar DSS Ta Saki Tsohon Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa

Da yake magana da ‘yan jarida ta wayar tarho, Timothy Adokwe, dan uwa ga Comfort, ya tabbatar da sakin nata inda yace an saketa da misalin karfe 8:30 na daren jiya.

Ya ce tun da farko masu garkuwan sun bukaci a biya su Naira miliyan 100 wanda ‘yan uwar malamar suka nuna cewar basuda su.

Advertisement

Ya tabbatar da cewa dangin sun biya kudin da ba a bayyana adadinsu ba domin ta sami ‘yanci.

Timothy, ya yabawa sojoji da kuma hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, kan hannun da suka yi wajen ganin an sako ‘yar uwar sa, inda ya ce duk da cewa ba za su iya matsawa kusa don gujewa cutar da Comfort ba, amma sun sanya ido ta hanyar tauraron dan adam.

A gaskiya ‘yan sanda ba sa nan, amma sojoji da DSS ne suka shiga dumu dumu amma a wajen domin sun yi kokarin sanya ido daga tauraron dan adam sun san wurin, amma ka san ba za su iya shiga kai tsaye ba kawai inji shi.

 

A wani labarin kuma Hukumar DSS Ta Saki Tsohon Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending