Connect with us

News

Yan Sandan Jihar Gombe sun kama wata mata bisa zargin ta da kashe mijinta ta  da tabarya.

Published

on

DAGA MUHAMMAD ZAHRAD

 

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wata mata mai suna Biba Mohammed bisa zargin ta da kashe mijinta ta hanyar yi masa rotse da tabarya.

Rahotanni na nuni da cewa an zargin matar mai matsakaicin shekararu ne wacce ke zaune ne a unguwar Barundare a garin Gombe, babban birnin Jihar da kashe mijin nata mai suna Muhammad Maliki.

Hukumar NIS tabbatar da cewa jamianta 4 sun rasu yayin da wasu 7 suka samu raunuka a wani hadarin mota a Kano

Rundunar ce ta sanar da kamun ta bakin Kakakinta, ASP Mahid Mu’azu Abubakar a madadin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Hayatu Usman.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 16 ga watan Nuwamban 2023 da misalin karfe 8:21 na dare.

Advertisement

A cewar sanarwar, “Jami’anmu sun samu kiran gaggawa a unguwar Barunde cewar an samu wani ta’asa a wani gida inda ake zargin natar gidan ta kashe mijinta.”

Kakakin rundunar ya ce nan take jami’an su da ke ofishin ’yan sanda na unguwar Low Cost da ke bangaren sashin bincike suka garzaya inda suka tarar da mai gidan kwance male-male cikin jini, inda suka yi gaggawar kai shi asibitin kwararru na Gombe, inda a can likita ya tabbatar da mutuwarsa.

A cewar ’yan sandan, binciken da suka gudanar a lokacin ne ya kai su ga samun nasarar kama matar, wacce suka ce ta amsa cewa ita ta kashe mijin nata.

Sanarwar ta kara da cewa a jawabin Biba da suka dauka ta shaida musu ita ta kashe mijin nata ta hanyar buga masa tabarya a ka, har ya mutu.

Sannan suka ce suna kan ci gaba da gudanar da bincike kuma da zarar sun kammala za su tura ta kotu.

Aminiya ta ruwaito cewa Biba ta ce ta yi nadamar matakin da ta dauka a kan mijin nata.

Advertisement

A wani labarin kuma Yan Sandan Jihar Gombe sun kama wata mata bisa zargin ta da kashe mijinta ta  da tabarya.

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending