Connect with us

News

Yan Sanda Sun Kama Wani Mai Kwacen Waya Da  Ya Guntule Yatsun Matashi 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

’Yan sanda sun cika hannu da wani mai kwacen waya da ya guntule wa wani matashi yatsu biyun hannunsa a garin kwace masa waya a Abuja.

Advertisement

An cafke mai kwacen wayan ne bayan wannan aika-aka da ya yi wa makiyayin mai shekaru 18 a unguwar Lugbe.

Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Gidauniyar Tallafawa Iyalan Sojojin Da suka Rasu

Rahotanni na nuni da cewar Bayan dawowa daga kiwo ne matashin mai suna Saleh Ibrahim ya je karbo wayoyinsa a wurin masu caji, inda a hanyar dawowa wanda ake zargin ya far masa, ya sare shi a kai.

Advertisement

Kawun Saleh ya ce mai kwacen wayan na neman sake sarar Saleh a kai ne Saleh ya sa hannunsa domin karewa, nan take mai kwacen ya guntule masa yatsu biyu.

A cewarsa, “Sai ya zubar da duk wayoyin biyu don ya ceci rayuwarsa, ya dawo gida, aka kai shi asibiti, yanzu haka an kwantar da shi.

Advertisement

“Mun sanar da ’yan sanda a caji ofis na Tudun-Wada a Lugbe, suka kira ofishin ’yan banga na kauyen Jiddu, suka kamo wanda ake zargin.

Mun nemi karin bayani daga kakakin ’yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, amma ta ce za ta bincika, in ya so daga baya ta yi bayani.

Advertisement

A wani labarin kuma Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Gidauniyar Tallafawa Iyalan Sojojin Da suka Rasu

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending