Connect with us

News

Tsadar Kayan Abinci: Gwamna Abba Kabir Yusuf Zai Nemi  Taimakon Shugaba Tinubu

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano yace zai roki shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya sa baki domin nemo mafita kan magance matsalar yunwa a jihar.

“Mun san cewa, sauran sassan kasar nan suna fuskantar irin wannan kalubalen, amma jiharmu ce a gabanmu farko,” inji shi.

Lokaci Yayi Da Za’a Kawo Karshen Musgunawa Fulani – Dakta Awwal 

Rahotanni na nuni da cewa lamarin ya yi kamari, don haka dole ne Gwamnatin Tarayya ta sa baki don fitar da jama’a daga halin da ake ciki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da ‘yan kasuwar jihar a dakin taro na Africa House da ke gidan gwamnatin Kano a ranar Litinin.

An kira taron ne a karo na biyu, domin tattauna halin da ake ciki a harkokin kasuwanci, musamman a kan tsadar kayayyaki, da nufin samar da mafita ga matsalar.

Advertisement

Gwamnan ya koka da yadda ake fama da matsalar yunwa a jihar, inda jama’a musamman talakawa ke gaza cin abinci a kalla sau uku a rana.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending