News
Masu garkuwa da mutane na amfani da macizai masu dafi domin tsorata mu —Mutanen da suka shaƙi iskar ‘yanci
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mutanen da suka shaƙi iskar ‘yanci daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su sun bayyana cewa mutanen da suka sace sun a amfani da macizai masu dafi domin tsorata su.
Wasu a cikinsu da suka bayyana halin da suka tsinci kansu a ciki a hirar da suka yi lokuta daban-daban da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN sun ce akwai macizai masu tarin yawa a cikin dajin da ‘yan bindigar suka mamaye.
Kanawa sun nuna damuwarsu kan sakin Murja Ibrahim Kunya ba tare da bayyana sharuddan belin ta ba
Sun ce macizan suna yawan sarar masu garkuwar da mutanen da aka sace.
Ɗaya daga cikin mutanen da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa NAN cewa masu garkuwar sun jefa su cikin matattarar macizai.
“Masu garkuwar sun san wuraren da macizai suke kuma suna ajiye mutanen da suka sace a nan.
“Da zarar sun ga macizai, masu jin tsoronsu sai su yi ta neman guduwa. Ganin macizan na tsoratar da su.
“Lokacin ne waɗanda aka sace suke neman ‘yan uwa da abokan arziki su sayar da komai – gida da fili da motoci da kayan gida da takalma, komai ma – kawai don a haɗa kuɗin fansa.”
Binciken da NAN ya yi ya gano dazukan da ke da mafi yawan macizai suna Birnin Gwari a jihar Kaduna da Kala-Balge kusa da tafkin Chadi a jihar Borno.
Wasu yankunan sun haɗa da Shaki a jihar Oyo da Borgu da Kagara a jihar Neja sai Karim Lamido a Adamawa da Lau a jihar Taraba.
Wasu cikin mutanen da suka kuɓuta daga hannun ‘yan bindigar sun shaida wa NAN cewa lamarin ya ƙazanta a yanzu ganin yanayin zafin da ake ciki yayin da macizan ke barin ramukansu da nufin neman abinci da shan iska.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
