News
Kotu Taki Amincewa A Saki Bayanan Kaddarorin Buhari Da Jonathan
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta yi watsi da daukaka karar bukatar sako bayanan kadarorin tsofaffin shugabannin Najeriya, da suka hada da Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari da mataimakansu Namadi Sambo da Yemi Osinbajo.
Punch ta ruwaito cewa wasu kungiyoyi biyu ne su ka rubutawa hukumar da’ar jami’an gwamnati CCB ta fito da bayanan bisa dokar ‘yancin samun bayanai ta 2011.
Kin fidda bayanan ya sa kungiyoyin shigar da karar bukatar tilastawa hukumar ta saki bayanan.
Bayan rashin nasara a babbar kotun tarayya, daya daga kungiyoyin ta daukaka kara, amma nan ma kotun ta ce ba zai yiwu a saki bayanan ba, ba tare da tsari daga majalisar dokoki ba kamar yadda yake a tsarin mulki.
Haka zalika Muryar Amurka ta ruwaito cewa kotun ta ce da karar Majalisa ya dace a shigar don tilasta ta sako tsarin don samun hurumin fidda bayanan.
Mai daukaka karar Chido Onuma ya ki amincewa da hukuncin yana mai alwashin garzayawa kotun koli.
Onuma ya zargi sashen shari’a da kawo tarnaki a samun bayanai daga gwamnati.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
