News
Muna Kokarin Ganin An Shawo Kan Matsalar Ruwa A Asibitin Kwararru na Murtala – Dr Nagoda
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Sakataren zartarwa na hukumar kula da asibitocin jihar Kano Dakta Mansur Mudi Nagoda ya yi kira da jama’a da su kara hakuri domin hukumar na kokarin ganin an shawo kan matsalar samar da ruwan sha a asibitin kwararru na Murtala Muhammad.
Dokta Nagoda ya yi wannan roko ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a ranar Larabar da ta gabata inda ya bukaci gwamnati ta samar da wasu hanyoyin da za a samu ruwa a Asibitin.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da jami ar yada labarai ta Hukumar Samira Suleiman ta turawa da Jaridar Inda Ranka
Sanarwar ta karada cewa a halin yanzu, akwai rijiyoyin burtsatse guda 12 a cikin ginin amma saboda girma da kuma sauyin yanayi ruwan ba ya iya kaiwa.
Ya kara da cewa, “domin a samu saukin lamarin, za mu rika samar da tankokin ruwa guda biyu a kullum, 1 za a ajiye a sashin haihuwa, daya kuma a sashin yara .”
Bugu da kari, sakataren zartaswar ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta samar da karin rijiyoyin burtsatse a cikin Asibitin
Haka zalika ya jaddada cewa hakan zai kara saukaka matsalar rashin isasshen ruwan sha a cikin Asibitin.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
