News
Majalisar Dattawa Ta Amince Wa Tinubu Ciyo Bashin $500m Don Sayen Mitocin Lantarki
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciyo bashin Dala miliyan 500 da nufin samar da mitocin wutar lantarki ga ’yan Najeriya.
A zaman majalisar na ranar Labara ne ta amince wa Shugaba Bola Tinubu ya karbo bashin daga Bankin Duniya.
Majalisar dattijan Najeriya na so a bai wa ƙananan hukumomi ƴancin kansu
Bayan karbar rahoton kwamitin basukan kasashen waje ne majalisar ta amince da karbo bashin wanda za a damka ga Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE).
Bashin Dala miliyan 500 da za a sayi mitocin lantarkin da su wani bangare ne na bashin Bankin Duniya na Dala biliyan 7.94 da Tinubu ya samu anincewar majalisar da zai karbo a karkashin tsarin karbar basukan kasashen waje na 2022-2024.
Da yake gabatar da rahoton, mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Haruna Manu, ya ce kudaden da mitocin za su taimaka wajen ingata samun wutar lantarki a kasar.
A cewarsa, aikin samar da mitocin zai kara ingantar karfin kamfanonin rarraba wutar lantarki da kuma samun kudaden shiga a gare su.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
