News
Sanata Ndume Da Kungiyar Kwadago Sun Aika Muhimmun Sako Ga Shugaba Tinubu A Kan Shirin Zanga-Zangar Matasa
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Tsohon mai tsawatarwa a zauren majalisar dattijai, Sanata Ali Ndume, ya roki shugaban kasa, Bola Tinubu, ya saurari kuka da korafin ‘yan Nigeria dake shirin gudanar da zanga-zanga.
Sanata Ndume ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a wani shiri na siyasa a gidan Talabijin na Channel a ranar Litinin.
Muhimman Abubuwa Shida Dangane Da Tababar Da Ta Barke Tsakanin Dangote Da Gwamnatin Shugaba Tinubu
Kafafen yada labarai sun rawaito cewa daruruwan ‘yan Nigeria na cigaba da yin shirin gudanar da zanga-zanga a dukkan jihohi 36 domin nuna fushinsu a kan halin matsin rayuwa da ake fama da shi a kasa.
Shi ma, a nasa bangaren, shugaban kungiyar kwadago a Nigeria (NLC), Joe Ajaero, ya yi kira ga shugaba Tinubu a kan ya nemo shugabannin zanga-zangar da ake shiryawa domin tattaunawa da su.
Ajaero ya bukaci Tinubu ya saurari kukan jama’a tare da bayyana cewa miliyoyin ‘yan Nigeria basa farinciki da halin tsananin rayuwar da suke fama da shi.
A cewar Ajaero, lamarin matsin rayuwa ya kai ga wasu iyalan da yawa basa iya samun abincin da zasu ci koda sau daya a rana.
A yayin da aka tambayi Ndume ra’ayinsa a kan kalaman Ajaero, ya bayyana cewa shi ma ya amince kan cewa akwai bukatar shugaba Tinubu ya saurari masu shirin gudanar da zanga-zangar.
“Ina goyon bayan wanan kira. Shugaban NLC ya fadi gaskiya. Ina goyon bayansa a kan cewa akwai bukatar shugaban kasa ya saurari bukatar ‘yan Nigeria”, a cewar Ndume.
Kazalika, Nudme ya bayyana cewa ba yanzu ne lokacin da ya dace a yi zanga-zanga ba saboda ana cikin yanayi na barazanar tsaro da ya hana manoma da yawa noma gonakinsu a sassan arewa, musamman jihar da ya fito, jihar Borno.
Ndume ya kara da cewa yana fargabar kada abinda ya faru sakamakon zanga-zangar ‘END SARS’ ya sake faruwa a wannan karon, yana mai bayyana cewa yana da yakinin cewa shugaba Tinubu zai magance matsalolin Nigeria idan aka bashi lokaci.
