Connect with us

News

Sai Nan Da Shekaru Hamsin Za A Fara Gudanar Da Sahihin Zabe A Najeriya —Farfesa Manunfashi

Published

on

Sai Nan Da Shekaru Hamsin Za A Fara Gudanar Da Sahihin Zabe A Najeriya —Farfesa Manunfashi

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaban Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Jihar Kano KANSIEC, farfesa Sani Lawan Manunfashi ya ce sai nan da shekaru 50 yake tunanin za,a fara gudanar da sahihin Zabe a Najeriya.

Farfesa Manunfashi ya bayyana haka ne a cikin Shirin Bakon mako na Tashar Dan Uwa Rano TV dake akan manhajar YouTube .

Hukuncin Da Ministan Ilimi Ya Dauka Na Haramta Digirin Benin Da Togo Ya Sabawa Ka’ida -Jami’ar Iheris 

Farfesa Manunfashi ya ce idan har aka cigaba da tafiya a haka sai Gwamatin tarraya ko jiha ce zata baiwa hukumomin Zabe kudaden da zasuyi amfani dasu wajen gudanar da harkkokin Zabe tom dole ne a cigaba da samun matsalolin da dama domin baza,a tabayin sahihin Zabe ba.

 

Haka zalika a lokacin da Farfesa Manunfashi ke amsa tambayoyin akan tsadar kudin form din Yan Takarar Shugaban Ƙaramar hukuma akan Naira Miliyan 10 da kuma na kansila akan Naira Miliyan 5 da Hukumar ta sanyawa kowanne dan Takara.

Advertisement

Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa akan haka ne Ƙungiyoyin faran hula da kuma Jamiyyun Adawa keta korafe korafe tare da zargin Hukumar KANSIEC da bude sabon shafin baraka wajen karuwar cin hanci da rashawa a akan yan siyasar jihar Kano.

Sai dai Farfesa Manunfashi ya ce ya za ma tillas Hukumar KANSIEC ta sanya wadannan kudade ga kowanne dan takara domin samun Inganci wajen biyan ma,aikatan da suka kula da Zabe a Wannan lokacin saboda babban ci da aka samu na tsarin tattalin Kasa.

 

Farfesa Manunfashi ya ce akwai bukatar Gwamnati Tarraya ta samar da hukumomi da zasu zama masu zaman kansu da zasu saka ido akan Inganci da Kuma bibiyar Al,amaran Zabe domin samun cigaba mai Inganci.

Haka zalika ya ce Hukumar KANSIEC a shirya take wajen gudanar da sahihin Zabe mai Inganci matukar wasu yan siyasa bazasu shigo sun bada matsalaba wajen baiwa talakawa taliya da Sabulu a lokutan Zabe Kuma jamian tsaro zasu gudanar da aikinsu bisa tsari da gogewa.

Wannan dai na zuwa ne dai dai lokacin da hukumar ke shirin gudanar da Zaben Kananan hukumomin a watan Nuwambar dake tafe.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending