News
Man Fetur Din Dangote Zai Fara Isa Kasuwa Makon Gobe – Kamfanin NNPC
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kamfanin man fetur din Najeriya (NNPC) ya bayyana cewa man fetur din matatar Dangote zai fara isa kasuwa tun daga ranar 15 ga watan Satumba mai kamawa.
Kamfanin wanda ya bayyana hakan a sanarwar da babban jami’in yada labaransa, Olufemi Soneye ya fitar a jiya Alhamis a Abuja, tace kasuwa da kanta ce zata yanke farashin da za a sayar da man.
Hakan dai ya biyo bayan fara tace man fetur din da matatar ta Dangote tayi a farkon makon nan.
Da yake ruwaito kalaman mataimakin shugaban bangaren cinikayyar albarkatun man kamfanin NNPC, Adedapo Segun, Soneye yace an kammala cefanar da bangaren cinikayyar kamfanin don haka bashi da sauran hakkin yanke farashi.
Kalaman nasa sun kawo karshen rade-raden da ake yi na cewar NNPC zai cigaba da yanke farashin albarkatun man fetur
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
