Connect with us

News

Kamfanin NNPCL Zai Fara Lodin Man Fetur Daga Matatar Dangote Ranar 15 Ga Satumba

Published

on

Matatar Man Dangote ta zargi hukumar NUPRC da gazawa wurin gudanar da ayyukanta
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa a ranar Lahadi 15 ga Satumba za a soma lodin kashi na farko na man fetur daga matatar mai ta Dangote da ke Jihar Legas.
Kwamitin shugaban kasa kan sayar da ɗanyen mai ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a a Abuja.
Shugaban hukumar tattara haraji na Najeriya Zach Adedeji wanda mamba ne a kwamitin ya bayyana cewa daga ranar 1 ga watan Oktoba, kamfanin na NNPCL zai soma bayar da ganga 385 ta ɗanyen mai a kullum ga matatar Dangote.
Ya ƙara da cewa ita kuma matatar ta Dangote za ta bayar da fetur da man dizel wanda ya zo daidai da darajar man a kasuwa kuma a biya kuɗin a naira.
An shafe lokaci ana kwan-gaba kwan-baya tsakanin kamfanin na NNPCL da kuma matatar ta Dangote dangane da batun ciniki da hada-hada ta ɗanyen mai.
Haka kuma duka wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu ƙarin kuɗin mai a Nijeriya, lamarin da ya ƙara saka ‘yan ƙasar da dama ƙorafi.
A farkon watan nan ne aka wayi gari gidajen mai mallakar kamfanin na NNPCL sun ƙara farashin da ake sayar da man fetur ɗin.
Sai dai jama’a da dama a faɗin ƙasar na fata za a samu sauƙin farashi idan matatar ta Dangote ta soma samar da man fetur a ƙasar.
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending