Connect with us

News

Gwamnatin Jihar Kano Ta Samu Bashin Naira Biliyan 177.4 Domin Samar Da Ruwan Sha A Jihar 

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano Ta Samun Bashin Naira Biliyan 177.4 Domin Samar Da Ruwan Sha A Jihar 
Gwaman Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Gwamnatin Kano ta samu bashin Naira biliyan 177.4 daga Hukumar Cigaban Faransa wato French Development Agency domin samar da ruwan sha a jihar.

Advertisement

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Ruwa na jihar, Alhaji Ali Haruna Makoɗa ya wakilta ne ya bayyana hakan a wani taron ƙara wa juna sani na kwana biyu da aka yi a Kano domin bibiya da tsara aikace-aikace wanda ya samu halartar wakilai daga jihohin Filato da Enugu da Ondo, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Biyan N77,000 A Matsayin Alawus Ga ‘Yan Yiwa Kasa Hidima NYSC

Ya ce aikin na samar da ruwan sha, yana cikin shirin inganta samar da ruwan sha na ƙasa, wanda ya samu sahalewar Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Najeriya.

Advertisement

Gwamnan ya ce an samu tsaiko ne a kan aikin ne tun bayan ɓarkewar annobar COVID-19 da wasu ƙalubalen, amma ya ƙara da cewa yanzu sun shirya cigaba da aikin, wanda ya ce za a kammala nan da shekara biyu.

Injiniya Garba Ahmad Bichi, Manajan Darakta na Hukumar Gidan Ruwan Kano ya ce aikin ya ƙunshi sake gina sabon hanyar adanawa da gyara ruwa wanda zai ɗauki lita miliyan 250 a kullum, wanda ya ce zai taimaka matuƙa wajen rage matsalar ƙarancin ruwa a jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending