News
Duk Ma’aikacin Da Bai Yi Rijistar Jiha Ba ,Ba Za Ta Ba Shi Albashi Ba —Gwamnati
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin jihar Kwara ta ce duk ma’aikacinta da bai yi rijista ya samu lambar hukumar rijistar mazauna jihar ba ba zai samu albashin watan nan na Nuwamba ba ko kuma alawus.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da kwamishinar kuɗi ta jihar Dr Hauwa Nuru ta fitar, mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta, a yau Litinin, inda ta buƙaci dukkanin ma’aikata na gwamnati da su tabbatar sun yi rajistar ba tare da ɓata wani lokaci ba.
Yan Arewa Basa Kalubalantar Dokar Ƙarin Haraji Da Shugaba Tinubu Zai Yi —Abdulmumin Kofa
Kwamishinar wadda ta ce tun a watan Yuli aka fara rijistar, ta ce gwamnatin jihar ta ɓullo da tsarin ne domin tattara bayanai a kan dukkanin mazauna jihar domin inganta tsare-tsare da ɗaunin albarkatunta da gudanar da ayyuka da tabbatar da lafiyar jama’a da sauran muhimman abubuwa.
Dr Hauwa ta ƙara da cewa rijistar, muhimmin mataki ne wajen samar da cikakken rumbun bayanai, da zai taimaka wa gwamnatin jihar wajen gudanar da harkokinta yadda ya kamata tare da tabbatar da gaskiya da amana tsakaninta da jama’a kamar yanda BBC HAUSA ta ruwaito
