News
Babbar Magana: An Kama Lauyan Bogi Ana Tsaka Da Shari’a A Kotu
DAGA MAIMUNA RABIU UMAR
Rundunar ƴansanda ta kama wani da ake zargin lauya na bogi ne mai suna Godwin Eguabor yayin da ya ke wakiltar wani mutum a wata kotu da ke jihar Legas.
Rahotanni na nuni da cewa Eguabor ya bayyana a gaban wata kotun majistare da ke yankin Badagry a Legas a ranar Laraba a matsayin lauya da ke wakiltar wani mai kara.
Wata Budurwa Ta Rasu Sanadiyyar Gobara Da Ta Kama Cikin Gidan Su A Kano
Atule Elchors, mataimakin shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Badagry, ya ce yayin zaman kotun a ranar Laraba, Eguabor ya bayyana kansa a matsayin lauya da ke wakiltar wani.
Elchors ya bayyana cewa ya dade yana jin jita-jitar wani lauya na bogi na gudanar da ayyukan lauya a yankin Badagry.
“Mun tambaye shi lambar kotun koli, wadda ita ce lambar rajista ta kowanne lauya, amma bai iya bayar da amsa ba, sai dai labaru marasa tushe ya ke ba mu.
“Abin takaici ma shi ne sunan da ya ke amfani da shi a kotu ya bambanta da sunan da ya ba wa ƴansanda lokacin da su ka kama shi.”
