Connect with us

News

Rundunar ’Yan Sanda Sun Kama Wani Mafarauci Bisa Zargin Tonon Kabari Da Yanke Kan Mijin Mahaifiyarsa.

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mafarauci mai shekara 55 mai suna Yusuf Garba, wanda aka fi sani da Gana, bisa zargin tona kabari tare da yanke kan mijin mahaifiyarsa.

Advertisement

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa a lokacin da ake masa tambayoyi.

Matatar Man Fetur ta Dangote Ta Rage Farashin Fetur

Garba, wanda ɗan asalin garin Tappare Kona Uku ne a ƙaramar hukumar Jada, ya bayyana cewa ɗan marigayin ne ya tuntuɓe shi inda ya buƙaci kan mijin mahaifiyarsa domin yin tsafi bayan rasuwarsa.

Advertisement

Rundunar ’yan sanda ta ce bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike. Ana kuma jan hankalin jama’a da su ci gaba da ba da hadin kai ga jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da bin dokaa jihar.

 

Advertisement

 

ALBARKA RADIO

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending