Business
Dillalan Man Fetur A Fadin Kasar Sun Koma Hulda Da Matatar Dangote Bayam Sun Fara Yanke Alaka Da NNPC
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wasu ‘yan kasuwar man fetur a sassan fadin kasar nan sun fara canza tambarin kamfanin man fetur na kasa NNPCL a gidajen mansu a daidai lokacin da dillalan ke yanke hulda da NNPC saboda yadda ake gasa tsakanin NNPC da matatar man Dangote.
Jaridar Punch ta rawaito cewa daukar wannan mataki na fara kauracewa kamfanin NNPCL yafi tasiri a Jihar Lagos musamman a baya bayan nan da Dangote ya sake karya farashin litar man fetur.
Shugaba Tinubu Ya Nemi Majalisar Dattawa Ta Kore Wasu Kwamishinonin Zaɓe
Tuni wasu dillalan da ke da tambarin NNPCL a gidajen mansu a kusa da yankin Wawa a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, da kuma a Ibafo, da wurare da dama sun cire tambarin NNPCL daga gidajen man su da motocin dakon man fetur mallakinsu.
Wata majiya ta shaida cewa abinda yan kasuwa masu zaman kansu ke bukata a yanzu bai wuce samun isassun kayayyakin da za a samu a cikin farashi mai rahusa,ba musamman a yanzu da matatar Dangote ke yawan sauko da farashin litar man fetur fiye da NNPCL.
Har ila yau, an gano cewa da yawa daga cikin ‘yan kasuwa na iya cigaba da yanke hulda da NNPC saboda rage kudin lodin Man Fetur da matatar Dangote ke yawan yi lokaci zuwa lokaci fiye da kamfanin NNPCL.
Rahotanni sun bayyana cewa an sake samun sauyi da gasa a kasuwar man fetur bayan da matatar mai ta Dangote ta sake rage farashin man daga N950 zuwa 890 kan kowacce lita.
