News
KATSINA: Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 4, Sun Sace 45
Jama’ar ƙauyen Maikuma da ke cikin ƙaramar hukumar Dandume ta Jihar Katsina sun wayi gari cikin fargaba bayan wani mummunan hari da wasu ƴan bindiga suka kai a daren Lahadi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane huɗu tare da sace aƙalla 45 daga cikin mazauna yankin.
Shaidu sun bayyana cewa ƴan bindigar, waɗanda yawansu ya haura 100, sun mamaye ƙauyen ne dauke da muggan makamai, suna shiga gidaje daga layi zuwa layi tsawon awanni kafin su tsere da waɗanda suka sace zuwa dajin da ke kusa da yankin.
Duk da hanzarin jami’an tsaro, rahotanni sun nuna cewa ba su iya cimma nasarar kamo ƴan bindigar ba, yayin da suka fice daga yankin bayan kammala aika-aikarsu. Shugaban ƙaramar hukumar Dandume, Basiru Musa, ya tabbatar da faruwar harin, tare da bayyana damuwarsa kan yawaitar ire-iren waɗannan hare-hare da ke barazana ga rayuwar al’umma.
Saudiyya Ta Karyata Sanya Takunkumin Biza Ga Najeriya Da Wasu Ƙasashe 13
Musa ya yi kira ga hukumomi da su ɗauki tsauraran matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Sai dai zuwa yanzu hukumomin tsaro na Jihar Katsina ba su fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, lamarin da ke ƙara jefa al’umma cikin damuwa da rashin tabbas.
