News
Masu Hakar Ma’adinai Biyu Daga Kano Sun Rasu Sakamakon Ruftawar Rami A Neja
Hukumar ‘yan sanda ta jihar Neja ta tabbatar da mutuwar mutane biyu sakamakon ruftawar wani ramin hakar ma’adinai da ke yankin Farin-Doki, a karamar hukumar Shiroro.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana wa manema labarai a Minna cewa lamarin ya faru ne da daren Lahadi, inda ramin hakar ya rufta tare da rufe wasu ma’aikata biyu da ke aiki a wajen.
Masu hakar ma’adinai da suka rasa rayukansu sun kasance Buhari da Mallam Tasiu, dukansu ‘yan asalin jihar Kano ne, in ji jami’in.
Abiodun ya ce jami’an ‘yan sanda daga ofishin Erena tare da hadin gwiwar mazauna yankin sun gaggauta kai dauki, amma da aka iso wurin an tarar ramin ya rigaya ya rufta sosai.
Bayan wani lokaci ana tono, an ciro gawarwakin mutanen biyun, inda aka kai su asibitin Zumba domin gudanar da karin bincike.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana cewa an fara gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin faruwar lamarin da kuma matakan da za a dauka domin kauce wa irin haka a nan gaba.
