News
Yan Bindiga Sun Sace Masu Kai Amarya A Zamfara
‘Yan bindiga sun sace mata kimanin 27 da ke rakiyar kai wata amarya a kauyen Kumi a karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.
Rahotanni sun ce ‘yan bindiga ne suka tare su a hanya suka kuma yi awon gaba da su ba tare da bata lokaci ba.
APC Na Samun Gagarumar Goyon Bayan Kano Arewa Saboda Jiga-Jigan Siyasa Uku
Wani mazaunin yankin ya shaida wa sashen Hausa na BBC cewa, matan sun taso ne domin halartar wani bikin aure da ke wani kauye a makwabtaka da nasu, sai dai suka fada hannun masu garkuwa da mutane a tsakiyar hanya.
A wani lamari makamancin haka, wasu mutane 19 ne aka sace a garin Galadi da ke karamar hukumar Tsafe, inda maharan suka kai farmaki da dare. Wasu daga cikin mazauna yankin sun samu raunuka a yayin harin.
Wadannan hare-hare na baya-bayan nan sun sake tayar da hankalin al’umma a yankunan, inda jama’a ke kara shiga halin fargaba da damuwa.
Jihar Zamfara na daga cikin wuraren da ke fama da matsalar tsaro, musamman a yankunan karkara, inda ‘yan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare, sace mutane da kuma tilasta wa jama’a biyan kudin fansa.
DAILY POST
