News
‘Yan Bindiga Na Cin Karensu Babu Babbaka A Shanono Da Bagwai – Dan Majalisa
Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Ɓagwai da Shanono a Jihar Kano, Yusuf Badau, ya koka kan yadda ‘yan bindiga ke addabar yankin da yake wakilta.
PRNIGERIAN ta ruwaito cewa Yayin gabatar da kudiri a gaban Majalisar Wakilai ranar Talata, dan majalisar ya nemi karin jami’an tsaro domin magance hare-haren da ya ce sun dabaibaye mazabarsa.
Ya ce, “Ranar 17 ga Afrilu, ‘yan bindiga sun kai farmaki kasuwar garin Farin Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Shanono, inda suka kashe mutum biyu, suka jikkata shida, sannan suka sace mutum daya.”
Ya ce an sake kai wani hari a ranar 26 ga Afrilu a garin Shanono, amma mutanen garin sun tsaya tsayin daka suka kare kansu, suka kuma fatattaki ‘yan bindigar.
“A ranar 2 ga Mayu kuwa, ‘yan bindiga sun sake bayyana a Fafarawa da Sandamu da ke tsakanin Shanono da Bagwai, inda suka yi garkuwa da mutum daya, suka sace wayoyi da babura guda bakwai, amma babu wanda aka kashe,” in ji shi.
Bayan gabatar da kudirin, Majalisar ta mika batun ga kwamitinta na harkokin tsaro da na ‘yan sanda domin daukar matakin da ya dace.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
