Connect with us

News

Pakistan Ta Harbo Jiragen Yakin India Biyar, Ta Kama Sojoji Takwas

Published

on

Screenshot 2025 05 06 at 7.22.30 PM

Sojojin Saman Pakistan sun harbo jiragen yakin India guda biyar tare da kama sojojin ƙasar takwas, a wani sabon rikici da ya ɓarke tsakanin ƙasashen biyu.

Ma’aikatar Tsaron Pakistan ce ta bayyana hakan a wani jawabi da ta fitar, tana mai cewa an dauki wannan matakin ne bayan India ta harba makamai masu linzami cikin ƙasar Pakistan, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane takwas tare da jikkata wasu aƙalla 35, yayin da mutane biyu suka ɓace.

Advertisement

DA ƊUMI-ƊUMI: Pakistan Za Ta Dauki Fansa Kan Harin Sama Da India Ta Kai

Ministan Tsaron Pakistan, Khawaja Asif, ya ce jiragen yakin India guda biyar aka harbo, sannan aka kama sojojin India takwas, wadanda yanzu ke hannun jami’an tsaron Pakistan.

A cewar Ministan Watsa Labaran ƙasar, Attaullah Tarar, an harbo jirgin farko a garin Akhnoor da ke yankin Kashmir da ake taƙaddama a kansa. Jirgi na biyu kuwa an harbo shi a birnin Ambala na India, yayin da wani jirgin maras matuƙi aka harbo shi a yankin Jammu da ke ƙarƙashin ikon India.

Advertisement

“Mun mayar da martani ne bayan India ta kai hari da makamai masu linzami a yankunan fararen hula na ƙasar mu,” in ji Tarar cikin wata hira da gidan talabijin na TRT World.

Wani jami’in rundunar sojojin Pakistan ya ce sun lalata wasu kayayyakin tsaron India a wannan luguden.

Advertisement

Mazauna yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon India sun tabbatar da jin ƙarar fashewar abubuwa da kuma ganin sassan jiragen da aka harbo, inda suka fara yada bidiyoyi a kafafen sada zumunta.

Wannan rikici dai na zuwa ne a lokacin da dangantakar Pakistan da India ke ci gaba da fuskantar ƙalubale, musamman a kan rikicin yankin Kashmir.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending