News
UTME 2025: JAMB Ta Rike Sakamakon Dalibai 39,834
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare (JAMB) ta sanar da dakatar da sakin sakamakon jarrabawar UTME ta bana ga ɗalibai 39,834 saboda zargin aikata maguɗi da wasu matsaloli da suka taso.
Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudana a Abuja, inda ya ce an riga an saki sakamakon ga sama da ɗalibai miliyan 1.9 da suka zauna jarrabawar a fadin ƙasar.
Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Daukar Gidajen Rediyon Kano A Matsayin Matattarar Batanci
Ya ce daga cikin waɗanda aka dakatar da sakamakonsu, 96 an tabbatar sun yi maguɗi, lamarin da ya ragu idan aka kwatanta da mutum 123 da aka kama da irin wannan laifi a shekarar da ta gabata.
Farfesa Oloyede ya ƙara da cewa ɗalibai 2,157 sun fuskanci ƙin karɓar yatsunsu a cibiyoyin jarrabawa saboda sabanin bayanai da suka bayar lokacin rajista.
Haka kuma, hukumar ta kama ɗalibai 244 da ake zargi da shiga ƙungiyoyin WhatsApp da ke yaɗa tambayoyin jarrabawa, tare da haɗin gwiwar wasu cibiyoyi na CBT.
JAMB ta bayyana sunayen wasu daga cikin cibiyoyin da aka samu da hannu a harkar, tare da yanke hukuncin dakatar da su, yayin da aka maka mutum 80 kotu bisa zargin zamba da maimaita rajista.
Hukumar ta ce tana ci gaba da bincike don tabbatar da adalci ga waɗanda suka cancanta da hukunta masu laifi domin kare martabar jarrabawar.
