News
Kotu Ta Tura Matasa Gidan Yari Kan Yunkurin Hana Zance A Kano
Wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Shamsuddeen Ado Abdullahi Unguwar Gini, ta tura wasu matasa biyu gidan yari bisa zargin kai hari kan wani saurayi da ya je yin zance a unguwar Ja’en da adda.
Wadanda ake zargin, Usman Rabi’u Usman da Aliyu Rabi’u Usman, na fuskantar tuhuma ne daga Kungiyar Ci Gaban Al’ummar Ja’en, wadda ta shigar da karar bisa zargin cewa matasan sun ɗauki doka a hannunsu tare da kafa dokar hana yin zance a unguwar.
Lauyar gwamnati, Barista Aliya Aminu Yargata, ce ta gabatar da kara a gaban kotun, inda ta karanta musu tuhumar. Duk da cewa sun musanta laifin, lauyar ta nemi lokaci domin gabatar da shaidu a gaba.
Lauyan wadanda ake kara, Barista Jamilu Ja’afar, ya roki kotun da ta ba su beli, amma Mai Shari’a bai amince da bukatar ba.
Kotun ta umarci a tsare su a gidan yari har zuwa ranar 22 ga watan Mayu, domin ci gaba da sauraronshari’ar.
