News
NAFDAC Ta Rufe Wasu Shaguna A Kano, Ta Cafke Mutum 6 Kan Sayar Da Man ‘Bleaching’
Jami’an Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), reshen Kano, sun rufe wasu shaguna a kasuwar Sabon Gari, tare da kama mutane shida da ake zargi da laifin sayar da miyagun man gyaran fata da bai da sahalewar hukumar.
Shugaban hukumar a jihar, Kasim Ibrahim, ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa matakin ya biyo bayan korafe-korafe daga jama’a da suka kai koke ta kafafen sada zumunta.
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Kudirin Magance Matsalar Karancin Ruwan Sha
Ibrahim ya ce bisa wannan koke, hukumar ta kaddamar da bincike cikin sirri, inda ma ta sayi wasu daga cikin kayayyakin da ake zargi don gwaji.
“Mun gudanar da bincike, kuma mun tabbatar da cewa kayan suna dauke da sinadarai masu haɗari da ke barazana ga lafiyar masu amfani da su,” in ji Ibrahim.
Ya ce binciken ya gano cewa mutum shida na da hannu wajen rarrabawa da sayar da wadannan kayayyaki.
Ibrahim ya bayyana cewa mayukan da aka kama na kama da kayan kwalliya, amma suna dauke da sinadarai da ke haifar da illa ga fata, kuma hukumar ba ta amince da su ba.
Ya kara da cewa NAFDAC, tare da hadin gwiwar sashen bincike da aiwatar da dokoki, ta rufe shagunan da ake zargi da safarar kayayyakin, tare da kwashe su domin gudanar da gwaje-gwaje a dakin binciken hukumar.
Haka kuma, hukumar ta ce ta rufe wasu kamfanonin da ke kwaikwayon kayayyakin da aka riga aka yi wa rajista ko suka karya dokokin NAFDAC, har sai an kammala bincike.
Ibrahim ya bukaci jama’a da su kasance masu lura da kayayyakin da suke saya, tare da rokon su su rika sanar da hukumar idan sun gano wani abu da ya saba wa doka.
“Lafiyar jama’a na da matukar muhimmanci. Muna bukatar hadin kan kowa wajen dakile yaduwar irin wadannan kayayyaki,” in ji shi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
