News
Ruwan Sama Ya Rushe Gidaje Sama Da Dubu Daya A Kano
Akalla mutum uku sun rasa rayukansu, yayin da sama da gidaje 1,000 suka rushe sakamakon mamakon ruwan sama da iska mai ƙarfi da kankara da aka tafka a ƙaramar hukumar Kiru ta jihar Kano.
Ɗan majalisar jihar Kano mai wakiltar yankin Kiru, Usman Abubakar Tasi’u, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da ƙudurin neman ɗaukin gaggawa a zauren majalisar jihar ga waɗanda lamarin ya shafa.
Jami’an Tsaro Sun Bankado Miliyoyin Kuɗi Da Aka Ɓoye A Jaka A Filin Jirgin Sama A Kano
A cewarsa, ruwan saman wanda aka yi a makon da ya gabata ya fi shafar yankuna kamar Dan Soshiya, Gwadaki, Yako, Maraku, Barguni da Kiru — inda ya haddasa rushewar gidaje da asarar rayuka.
“Mutane da dama sun rasa matsugunansu, wasu sun samu raunuka sakamakon ruftawar gine-gine, kuma har yanzu ba a kammala tantance asarar dukiyoyi da kadarorin da aka yi ba,” in ji Tasi’u.
Har ila yau, ruwan ya haifar da katsewar wutar lantarki a wasu ƙananan hukumomi makwabta da suka haɗa da Rogo da Karaye.
Majalisar dokokin Kano ta nemi gwamnatin jihar da ta tura kayan agaji cikin gaggawa, domin tallafawa mazauna yankunan da lamarin ya shafa.
Majalisar ta kuma bukaci a gudanar da bincike kan girman barnar da aka yi, tare da tsarawa kan hanyoyin rage illar ambaliya a nan gaba.
