Connect with us

News

Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Mata Biyu Da Ake Zargi da Satar Atamfofi

Published

on

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja ta kama wasu matasa mata biyu da ake zargi da satar atamfofi guda 15 da wasu kayayyakin amfanin gida a Minna, babban birnin jihar.

Mai magana da yawun rundunar, SP Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Minna, inda ya ce an kama Jamila Nuhu, mai shekaru 23 daga unguwar Limawa, bisa zargin ta da hannu a satar kayayyakin.

‎Harkar Noma Na Fuskantar Kalubale A  Fadin Najeriya ‎

Abiodun ya ce kama Jamila ya biyo bayan korafi da wata mata ta shigar cewa kayayyakin gidanta na salwanta ba tare da wani bayyani ba.

“Binciken da muka gudanar ya nuna cewa Jamila na hada kai da wata kawarta mai suna Fatima Mohammed, ‘yar shekara 20 daga Angwan Daji. Itama an kama ta,” in ji Abiodun.

Rundunar ta ce an gano atamfofi guda 15 da wasu kayayyakin girki a wurare daban-daban a Minna da ma wasu da ke Jihar Kaduna, inda ake zargin an aika su ga ‘yan uwa da abokan arziƙi.

Abiodun ya kara da cewa ana cigaba da bincike, kuma da zarar an kammala, za a gurfanar da su a gaban kotu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending