Connect with us

News

An Gano Masana’antar Ƙera Makamai A  Filato

Published

on

Rundunar haɗin gwiwa da ke aikin samar da zaman lafiya a Jihar Filato, Operation Enduring Peace, ta sanar da gano wata masana’antar ƙera makamai a ƙaramar hukumar Barikin Ladi da ke Jihar Filato.

Kakakin rundunar, Samson Nantip Zhakom ýa sanar da cewar, a ranar 17 ga watan Satumba, 2025 ne rundunar ta samu wani rahoton sirri game da ayyukan da ake yi a masana’antar, wanda ba tare da ɓata lokaci ba dakarun rundunar suka kai samame ƙauyen da abin ke faruwa, har kuma aka samu nasarar kama mutum ɗaya, da wasu makamai.

Advertisement

Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar ’Yarta ’Yar Shekara 10 Kan Zargin Maita A Bauchi ‎

Ya ce, a sakamakon binciken da aka gudanar an gano bindigogi guda 12 da wata ƙaramar bindiga guda ɗaya, da kwasfon harsasai 19, nakiya guda ɗaya, rigar da jami’an tsaro ke sawa a matsayin garkuwa, rediyon oba-oba, da wani bokiti mai cike da magunguna, da wasu nau’in makamai daban-daban.

Rundunar ta kuma bayyana cewa, mutumin da aka kama da makaman na nan tsare a hannun ta, yayin da take cigaba da bincike, da kuma neman waɗanda suka tsere, domin gurfanar da su a gaban kotu.

Advertisement

Rundunar ta yi kira ga jama’a da su cigaba da ba da haɗin kai wajen samar da muhimman bayanai na gaskiya da za su taimaka wajen gano maɓoyar waɗannan ɓatagari da kama su, don rage yawaitar makamai a hannun jama’a, da magance matsalolin tsaro a Jihar Filato da Nijeriya baki ɗaya.

 

Advertisement

DAILY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending