News
Fiye da ‘Yan Mata 2,200 Suka Fuskanci Cin Zarafi A Cikin Shekara Ɗaya A Legas — Rahoto
Hukumar Kare Hakkokin Mata da Yara ta Jihar Legas, wato Domestic and Sexual Violence Agency (DSVA), ta bayyana cewa aƙalla ‘yan mata 2,213 ne suka fuskanci nau’o’in cin zarafi daban-daban tsakanin watan Satumba 2024 zuwa Agusta 2025.
Sakatariyar hukumar, Mrs. Titilola Vivour-Adeniyi, ce ta bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Legas a ranar Asabar, yayin bikin tunawa da rana ta musamman da ake warewa don jan hankalin jama’a kan matsalolin da ‘yan mata ke fuskanta.
Tashin Farashin Gas Ya Tilasta Wa ‘Yan Najeriya Komawa Amfani Da Gawayi
Ta ce wannan rana tana nufin ƙarfafa kira ga gwamnati da al’umma gaba ɗaya da su ƙara tashi tsaye wajen kare ‘yan mata daga duk wani nau’in cin zarafi, musamman a cikin gida da makarantu.
“A cikin shekara guda, mun ba da tallafi ga mutum 8,692 da suka tsira daga cin zarafi. Daga cikinsu, yara 3,629 ne, kuma kashi 60 cikin 100 daga cikinsu ‘yan mata ne — wato 2,213, yayin da sauran kashi 40 cikin 100 yara maza ne,” in ji Vivour-Adeniyi.
Ta ƙara da cewa, yara masu ƙasa da shekaru tara ne ke cikin mafi haɗari wajen fuskantar irin waɗannan matsaloli, abin da ya sa hukumar ke ba su kulawa ta musamman ta fannin ilimi da tunani.
Vivour-Adeniyi ta kuma bayyana cewa, a lokuta da dama, iyaye ko masu kula da yara ne suke aikata irin waɗannan laifuka, wanda hakan ke ƙara wahalar da yaki da cin zarafi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
