News
Jirgin Ruwa Dauke Da Fasinjoji 270 Ya Yi Taho-mu-Gama A Gabar Tekun Koriya Ta Kudu
Wani jirgin ruwan fasinja dauke da mutane 267 ya yi taho-mu-gama da wani tsibiri mai duwatsu da ke yankin Jindo, a Kudu maso yammacin zirin Koriya, yayin da yake kan hanyar daga tsibirin Jeju zuwa birnin Mokpo.
Hukumar tsaron gabar ruwan kasar ta tabbatar da cewa cikin mutanen da ke jirgin akwai fasinjoji 246 da ma’aikata 21. A cewar hukumar, an gaggauta tura jiragen ruwa kusan 20 da wani jirgin sama domin aikin ceto.
Kano Online Media Chapel Ta Yabawa Kamfanin Dala Food Nig Da Kamfanin POP Cola
Jami’an sun ce dukkan fasinjojin an kubutar da su lafiya, duk da cewa an gano wani rami a jikin jirgin. Sai dai ba a samu shiga ruwan teku ba, kamar yadda kamfanin labarai na Yonhap ya ruwaito.
Hotunan bidiyo da aka wallafa sun nuna fasinjoji sanye da rigunan rayuwa, suna jiran kwale-kwalen ceto a gefen jirgin.
Tsibirin Jeju, wanda jirgin ya taso daga gare shi, na daga cikin manyan wuraren yawon bude ido a Koriya ta Kudu, kuma gida ne ga dutsen aman wuta na Hallasan, wanda ya shiga cikin jerin wuraren tarihi na UNESCO.
Wurin da hatsarin ya faru yana da nisan kadan daga yankin da jirgin ruwan Sewol ya nutse a 2014, lamarin da ya lakume rayukan mutane sama da 300.
