News
An Biya Wanda Aka Daure Bisa Kuskure Diyar Sama Da Naira Biliyan 2
Gwamnatin jihar Bavaria a Jamus ta amince da biyan diyya kimanin Naira biliyan 2.2 ga wani mutum da ya shafe shekaru 13 a gidan yari bisa hukuncin kisan kai, kafin daga bisani kotu ta wanke shi bayan gano cewa an yi masa hukunci ne bisa kuskure.
Mutumin, Manfred Genditzki, tsohon mai kula da gine-ginen gidaje, an yanke masa hukuncin daurin rai da rai a shekarar 2010 bayan wata kotu a Munich ta same shi da laifin nutsar da wata tsohuwa daga Rottach-Egern a cikin bandaki a shekarar 2008.
An Biya Wanda Aka Daure Bisa Kuskure Diyar Sama Da Naira Biliyan 2
Sai dai jim kaɗan bayan yanke hukuncin, masanan binciken likitanci suka fara nuna shakku kan sahihancin laifin da aka ɗora masa. Zuwa shekarar 2018, wasu ‘yan majalisa a Jamus suka fara bayyana cewa akwai yiyuwar an yi masa hukunci ba bisa ka’ida ba.
A shekarar 2022, an saki Genditzki daga gidan yari, sannan a 2023 wata sabuwar shari’a ta wanke shi gaba ɗaya, inda kotu ta ce mutuwar tsohuwar ta faru ne sakamakon haɗari, ba kisan kai ba.
A jimlace, Genditzki ya shafe shekaru 13, kwana 4,916 a tsare.
Bayan fitowarsa daga kurkuku, Genditzki da lauyansa sun nemi diyya daga gwamnatin jihar Bavaria.
Inda Sun ƙi amincewa da buƙatar masu gabatar da ƙara da ke neman ya biya kusan Naira miliyan 170 a matsayin kuɗin ciyarwa da masauki yayin zaman kurkuku.
A ranar Laraba, Ma’aikatar Shari’a ta jihar Bavaria ta sanar da cimma matsaya na biyan euro miliyan 1.3, wanda ya kai kimanin Naira biliyan 2.2.
Sai dai ma’aikatar ta ce ba zai karɓi dukkan kuɗin ba, domin wani ɓangare zai shiga haraji, haka kuma za a cire kuɗin lauyoyi.
Gwamnatin jihar Bavaria ta ce wannan lamari ya sake tayar da muhawara kan sake duba dokokin biyan diyya ga mutanen da aka yi wa hukunci bisa kuskure a Jamus.
