Connect with us

News

Mahara Sun Sace Shanu Sama Da 100 A Borno

Published

on

Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun tare manyan motocin dakon shanu guda huɗu, inda suka wawuri shanu sama da 100 suka tsere da su zuwa cikin daji a jihar Borno da ke arewacin Najeriya.

Lamarin ya faru ne a kusa da garin Kareto, cikin ƙaramar hukumar Mobbar ta jihar.

Advertisement

Fasinjoji 80 Sun Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Tangarɗar Injin Jirgin Arik Air

Majiyoyi sun shaida cewa, maharan sun ɗauki kusan awa guda suna sauke shanun daga cikin motocin kafin daga bisani su ruga da su cikin daji. Duk da cewa motocin ba tare suka taho ba, sai da maharan suka jira har suka taru wuri guda kafin su kai harin.

Advertisement

Rahotanni sun ce direbobin motocin sun tsallake rijiya da baya ba tare da sun jikkata ko rasa rai ba.

An bayyana cewa motocin sun taso ne daga Damasak da nufin isa Maiduguri, amma ba su wuce tafiyar mintuna 30 ba kafin maharan su tare su.

Advertisement

Wannan hari na zuwa ne kwanaki biyu bayan wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram sun bankawa wasu motocin dakon kaya ɗauke da wake daga Munguno zuwa Maiduguri wuta.

Jihar Borno dai ta shafe shekaru tana fuskantar hare-haren mayaƙan Boko Haram da ISWAP, lamarin da ke ci gaba da haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a yankin.

Advertisement

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending