News
HARIN DAKARUN SOJIN SAMA: Mun Rufe Kasuwar Jilli Shekaru 5 Da Suka Wuce — Gwamnan Borno
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnati ta rufe kasuwar Jilli shekaru biyar da suka wuce saboda ana zargin ’yan ta’adda da masu taimaka musu na amfani da ita.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake martani kan harin jirgin sama da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 50 a ranar Asabar.
Gidauniyar Dr. Aminu Magashi Garba Tana Ci Gaba Da Tallafa Wa Gajiyayu A Kano
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, gwamnan ya ce an riga an haramta amfani da kasuwar, wadda ke kan iyakar Borno da Yobe, tare da wata kasuwa mai suna Gazabure saboda matsalolin tsaro.
Zulum, ya gargaɗi mazauna yankin da su guji taimakawa ko boye ’yan Boko Haram, ko ba su wani tallafi.
Ya kuma ce gwamnatin jihar na aiki tare da rundunar soji da gwamnatin Jihar Yobe domin magance lamarin.
Ya ƙara da cewa ana buɗe kasuwanni da mayar da mutane yankunansu ne kawai bayan an tabbatar da tsaro.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da haɗa kai da jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya.
Ya kuma buƙaci jama’a da su kasance masu lura tare da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa ayyukan da ake yi na tsaro.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
