News
Gwamantin legas Ta Kwace Babura Okada Sama Da 270
Jami’an Task Force na Jihar Legas Masu Yaki da Laifuffukan Muhalli da Sauran Take Dokoki sun sanar da kwace baburan Okada 278 a wani samame na mako guda da ta gudanar domin dakile masu karya dokar zirga-zirgar baburan haya a manyan tituna da hanyoyin da aka haramta.
Shugaban hukumar, CSP Adetayo Akerele, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Abdulraheem Gbadeyan, ya fitar a ranar Lahadi.
Yadda HE Garo Ya Wakilci Gwamna Fiye Da Wadansu Mataimakan Da Gwamnoninsu Cikin Kwanaki 47
A cewarsa, an gudanar da samamen ne bisa tanadin Dokar Gyaran Fannin Sufuri ta Jihar Legas ta shekarar 2018, wadda ta haramta zirga-zirgar baburan haya a wasu manyan tituna da wuraren da gwamnati ta ayyana.
Akerele ya ce matakin na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na inganta tsaro, kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da dakile ayyukan masu aikata laifuffuka.
Rahotanni na nuni da cewa gudanar da aikin a yankuna da dama da suka hada da Ikorodu, Festac, Iyana-Iba, Egbeda, Iyana Ipaja, Ikotun da Berger, inda jami’an hukumar suka kama masu Okada da dama suna aiki a wuraren da doka ta hana su.
Hukumar ta kuma ce wasu daga cikin wadanda aka kama suna jigilar kayayyaki masu hadari kamar man fetur da silindar gas, yayin da aka samu wasu suna daukar yara kanana a manyan hanyoyi ba tare da kiyaye ka’idojin tsaro ba.
