Connect with us

Sports

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta bayar da sanarwar naɗa Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles a wannan Laraba.

Published

on

Spread the love

Hukumar ta ce Jose Peseiro wanda ɗan asalin ƙasar Portugal ne shi zai maye gurbin Gernat Rohr da ta kora.

Tuni NFF ta naɗa Augustine Eguavoen a matsayin kocin rikon kwarya domin ya ja ragamar Super Eagles a yayin da ake shirin soma gasar cin kofin Afirka.

A cikin sanarwar da ta fitar NFF ranar Laraba ta ce kwamitin zartarwata ne ya amince da naɗa Peseiro ne bayan raba gari da Mr Gernot Rohr.

Advertisement

“Kwamitin ya amince Augustine Eguavoen a matsayin kocin riƙon ƙwarya ya jagoranci Super Eagles a gasar cin kofin Afrika Afcon 2021 a Kamaru yayin da kuma Mr Peseiro zai zama mai sa ido.”

Jose Peseiro wanda tsohon kocin ƙungiyar Sporting Lisbon da Porto ne, ya horar da Venezuela da Saudiyya.

Advertisement
  • Ya horar da ƙungiyoyi a Afirka da ƙasashen Larabawa da suka haɗa da Al ahly ta Masar da Al Hilal ta Saudiyya.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *