Connect with us

Sports

Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Aubameyang, Haaland, Luiz, Icardi, Coutinho

Published

on

122561655 gettyimages 1231165594.jpg
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Newcastle ta tuntuɓi Arsenal kan ba ƙungiyar aron Pierre-Emerick Aubameyang, dan wasan gaba mai shekara 32 da ke fuskantar matsala da kocinsa Arteta. (Sunday Mirror)

Kungiyar Newcastle – wadda ake kira Magpies – na son biyan fam miliyan 50 domin dauko Darwin Nunez, dan wasan gaban Benfica dan kasar Uruguay mai shekara 22. (The I)

Advertisement

Barcelona ta yi wa Everton tallan Philippe Coutinho, dan wasan tsakiya mai shekara 29 kuma koci Rafael Benitez na son dauko Nathan Patterson dan wasan Rangers da kasar Scotland mai shekara 20. (Mail on Sunday)

Arsenal ta nuna sha’awarta ta daukan Douglas Luiz, dan wasan tsakiya mai shekara 23 dan Brazil daga Aston Villa. (Sun on Sunday)

Dan wasan gefe na Aston Villa da kasar Netherlands Anwar El Ghazi mai shekara 26 na iya komawa West Ham da zarar an bude kasuwar cinikin ‘yan wasa a wannan watan na Janairu. (Football Insider)

Advertisement

Leicester na son raba kungiyar Vitoria Guimaraes ta Portugal da Abdul Mumin, dan wasanta na baya mai shekara 23. (Mail on Sunday)

Dan wasan gaba na Borussia Dortmund da Norway, Erling Braut Haaland mai shekara 21 ya shaidawa masu bibiyarsa cewa nan gaba zai taka tamaula a kasar Sfaniya. (AS – in Spanish)

Liverpool za ta dauki saboon dan wasan gaba a wannan watan na Janairu idan ta sami damar daukan dan wasan da zai jima a kungiyar. (Fabrizio Romano via Anfield Watch)

Advertisement

Dan wasan gaba na Paris St-Germain da Argentina, Mauro Icardi mai shekara 28 na iya komawa Juventus a matsayin dan aro na wata shida. (Pedro Almeida on Twitter)

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *