News
Gwamnatin Bauchi Za Ta Aurar Da Tubabbun Karuwai Guda Dari

Daga sahibu sale
Gwamnatin jihar Bauchi za ta aurar da tubabbun karuwai akalla 100 daga kananan hukumomi 20 dake jihar amma sai an kammala koyar dasu sana’o’in dogaro da kai daban-daban.
Sai dai wadanda suka tuba suka watsar da sana’ar ta karuwanci suka mika kansu ga Hukumar Hisba ne kadai zasu ci gajiyar wannan shiri.
Muryoyi ta ruwaito a ranar Talata Gwamnatin Bauchi ta yi wani shiri na koyar da sana’o’in hannu ga tubabbun karuwan su 575.
Sana’o’i da ake koya masu tare da hadin guiwa da hukumar samar da ayyukan yi ta kasa NDE, sun hada da harkokin kasuwanci, Ilimin sarrafa kwamfuta, Gyaran kai, kitso, saka da Dinki.
Sauran Sana’o’i sun hada da Kwalliya (makeup), sana’ar hada abinci (catering), kiwon kaji da kiwon kifi hada takalma da jakka da sauransu.
Hukumar ta yabawa matan da suka mika wuya daga wannan kazamar rayuwa ta bin maza wacce ke da hadarin gaske duniya da lahira.
Gwamnatin Bauchi ta ce zata dauki dawainiyar aurara da tubabbun matan da zaran an kammala koyar dasu sana’o’i, kuma Gwamnatin ce zata dauki duka hidimar auren sannan za a sanar da karin bayani kan ranar daura auren.