Interview
INA YAN ALUTA SHUWAGABANIN DALIBAN JAMI, A DAN GANI DA YAJIN AIKIN DA A KEYI NA TSAWAN WATANNI
Shugabannin dalibai na makarantun Jami,a (Students Union) su na gudun mawar da za su iya bawa yan uwan su dalibai dan ganin an magance wannan matsalar ta yajin aiki da akeyi a makarantun Jami a dake kasar nan.
Andauki lokaci mai tsayi a na yajin aiki a makarantun wanda har yanzu ankasa shaho kan matsalar.
Duba da Darajar da matasa su ke da ita a idan duniya, da,ace shugabannin daliban za su hadakai batare da sun ta da hayaniya ba ko kuma tozarma su kuma kau da duk wani abu da ze furgita mutane ko wata alama dake nuna fitina a idan jama, a su kuma yi amfani da yawan su da hadinkan su su futo zaga gari akalla su Tara motoci kamar guda dari a kowace jaha tare da rakiyar ma su babura kuma koda daliban jaha daya ne su ka gwada yin wannan ina da tabbacin ba ze tafi a banza ba.
A wadan su kasashen a kan rayuwar daidaikun matasa da ba su huce a kirga su ba majalisar dinki duniya ta na dakatar da wadansu abubuwan da yashafi kasar haka kuma ana iya janye mu su wadan su tallefe tallefe daga kungiyoyin duniya, amma mu kuma anan rayuwar dubban matasa aka dakatar.
Duba da wannan dalilin na ke kira ga yan gwagwarmayar dalibai da su futo kwansu da kwarkwatar su domin manema labarai su dauka su watsa duniya ta gani, sai mu ga idan yajin aikin za a cigaba da yi.
Daga. Amb Abba Alra-iwas
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
