News
Sudan ta Kudu mai fama da rikicin kabilanci ta jinkirta zaɓe
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugabannin Sudan ta Kudu sun sanya hannu a kan wani shiri, da zai kara wa’adin mulkin gwamnatin rikon kwarya da ke cikin yarjejeniyar zaman lafiya ta wata 24
Karin zai fara ne daga ranar 22 ga watan Fabrairu na shekara mai zuwa, 2023.
Tsohon Babban Sufeton ‘Yan-sandan Najeriya Tafa Balogun ya rasu
Shugaba Salva Kiir da tsohon abokin hamayyarsa, Riek Machar, wanda yanzu shi ne mataimakin shugaba da wasu manyan ƙusoshi sun rattaba hannu a kan shirin a babban birnin Kasar, Juba yau Alhamis.
Wannan karin wa’adi na nufin Sudan ta Kudu ba za ta yi zaben da aka dade ana jira ba a watan Fabrairun shekara mai zuwa.
Sabuwar yarjejeniyar ta tanadi yin zaben a watan Disambar shekara ta 2024.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
