News
Yayin da ake shirin koma wa hutu, gwamnatin tarayya ta tsaurara tsaro a makarantu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin tarayya ta ce tana haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da ingantaccen tsaro a makarantu yayin da za a koma hutu a ranar 12 ga watan Satumba.
Karamin Ministan Ilimi, Goodluck Opiah ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai domin shirye-shiryen bikin ranar kare ilimi daga hare-hare ta duniya ta 2022.
‘Warr’: Ba zan ƙara cewa komai ba — Ado Gwanja
A tuna cewa a watan Yuli ne gwamnatin tarayya ta rufe Kwalejin Gwamnatin Tarayya, FGC, Kwali da sauran Makarantun Babban Birnin Tarayya, FCT, saboda fargabar harin ‘yan bindiga.
Ministan ya ce rufewar ba ta dindindin ba ce, don haka an kusa bude makarantu kuma FGC Kwali ma za ta kasance cikin shirin buɗe makarantun.
“Ma’aikatar, tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro za su kare makarantunmu gaba daya kuma hakan ba zai zama wani lamari da ba a sani ba.
“Ku tabbata cewa tsaron yaranmu yana da mahimmanci a gare mu,” in ji shi.
DAILY NIGERIAN
-
News7 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News4 days agoKotu Ta Daure Wani Limamin Masallacin Juma’a Wata 1 Kan Tura Bidiyon Tsaraici Ga Matar Aure A Kano
-
News6 days agoƘalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
