Connect with us

News

An Kashe Malamai 10, An Sace 50 A Wata 10 A Kaduna

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

’Yan bindiga sun kashe malaman makarantu 10, wasu 50 kuma na hannunsu a Jihar Kaduna, daga watan Janairu zuwa Oktoban 2022.

Advertisement

Kungiyar Malaman Sakandare da Firamare ta Kasa (ASUSS), Reshen Jihar Kaduna ta ce hakan ta faru da malaman makarantun ne a a kananan hukumomin Kachia, Chikun, Kagarko, Sanga da kuma Kaura a jihar.

Ma’aikata a Zamfara za su fara karbar albashin naira dubu 30

Advertisement

Shugaban ASUSS a jihar, Kwamred Ishaya Dauda, ya ce, “Matsalar rashin tsaro ta fi ritsawa da malaman sakandare, inda daga watan Janairu zuwa Oktoban 2022 da muke ciki, an kashe malamai sama da 10 wasu 50 kuma har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane. Dalibai da dama ma an yi garkuwa da su.”

A jawabinsa na Ranar Malamai ta Duniya ta 2022, Kwamred Ishaya Dauda ya yi kira ga jami’an tsaro da su yi mai yiwuwa wajen ceto malaman da ke hannun masu garkuwa da mutane.

Advertisement

 

Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa hadin gwiwarta da ’yan banga wajen samar da tsaro a makarantu da ke jihar.

Advertisement

“An girke ’yan banga akalla shida a kowace kamaranta da ke fadin jihar domin samar da tsaro da aminci ga malamai da dalibai.”

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin da ta bullo da shirye-shiryen da za su rage radadin hauhawar farashin kayan masarufi da kuma biyan hakkokin wadadna suka yi ritaya domin saukaka musu.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

DAILY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending