News
Gobara Ta Tashi A Hedikwatar Hukumar NYSC Da Ke Abuja
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An samu tashin gobara a hedikwatar hukumar masu yi wa kasa hidima dake birnin tarayya Abuja ranar Juma’a.
Hukumar ta ce ba a samu asarar rai ba sakamakon barkewar gobarar kwatsam domin ta takaita ne a hawa na uku na ginin bene mai hawa shida.
Takarar Gwamnan Kaduna: Kotu Ta Kori Karar Sani Sha’aban
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da manema labarai, Eddy Megwa, ya fitar ranar Juma’a.
Ya ce nan take ofishin babban birnin tarayya da na hukumar kashe gobara ta tarayya suka kashe gobarar a lokacin da lamarin ya faru da misalin karfe 07:30 na safe.
Megwa ya kuma ce benen da abin ya shafa na cikin tsare-tsare, bincike da kididdiga da kuma babban ma’aikata inda gobarar ta shafi wani daki ne kawai da na’urorin lantarki.
Ya ce, “An yi sa’a, ba a yi asarar rai ba kuma an kwashe dukkan muhimman takardu da gaggawa kuma an kiyaye su.
“Masu gudanar da shirin suna godiya sosai ga Ma’aikatar kashe gobara ta Tarayya da FCT saboda yadda suka mayar da martani cikin gaggawa wanda ya rage tasirin lamarin.
“Hukumar ta kuma yaba wa dukkan hukumomin tsaro bisa gagarimar rawar da suka taka a lokacin da lamarin ya faru.”
NAN
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
