Connect with us

News

Dan Dambe Ya Mutu Bayan An Yi Masa Mahangurba

Published

on

Wani dan dambe ya gamu da ajalinsa a filin dambe, bayan da bayan da abokin karawarsa ya yi masa wawan naushi a haba.

 

Advertisement

Hukumar Shirya Wasanni ta Kasa ce ta shirya gasar a karo na 21 a Asaba a Jihar Delta, inda dan wasan mai suna Chukwuemeka Igboanugo ya rasa ransa, yayin da yake karawa da abokin dambensa.

 

Advertisement

zaiyi kokari wajen ganin an magance matsalar faduwa jarabawar daliban sharada.. -Abubakar Musa. 

Aminiya ta rawaito cewa an naushi Chukwuemeka ne a habarsa, inda ya fadi kasa warwas, ya kasa tashi wanda hakan ya sa alkalin wasan, ya ayyana abokin karawar tasa dan asalin Jihar Anambra a matsayin wanda ya yi nasara.

 

Advertisement

Sai dai daga bisani hankali ya tashi ganin dan damben ya kasa tashi, inda masu ba da agajin gaggawa suka garzaya da shi zuwa asibiti, amma likitoci suka ce rai ya riga ya yi halinsa.

 

Advertisement

 

Kakakin ’yan sandan jihar, Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba.

Advertisement

 

Yanzu haka dai, Kungiyar ’Yan Wasan Damben Najeriya da kuma Gwamnatin Jihar Delta ba su ce komai ba dangane da mutuwar dan damben.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending