Connect with us

News

Hatsarin Mota: Mutum 11 Sun Kone Kurmus A Hanyar Zariya Zuwa Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Wani mummunar hatsarin mota da ya auku a garin Marabar Gwanda da ke dab da shiga Zariya a hanyar Zariyan zuwa Kano ya yi sanadiyar konewar mata 11 kurmus.

 

Advertisement

Aminiya ta rawaito cewa  dukkan mutanen da suka rasu a hatsarin mata ne, kuma ya faru ne da yammacin ranar Asabar, tsakanin wata mota kirar Hilux da wata mai kirar bas.

 

Advertisement

DSS ta janye jami’anta daga tawagar Gwamna kan rashin jituwa da ‘yan sanda

Malam Abdul’aziz Isiyaku, mazaunin unguwar Tudun Jukun da ke Zariya, mahaifi ne ga yara biyu daga cikin mutanen da suka kone a hatsarin ya ce, “Dukkan wadanda suka kone mata ne kuma akwai ’ya’yana biyu; Zainab Abdul’aziz mai shekara 16 da kuma Aisha Abdul’aziz mai shekara takwas.”

 

Advertisement

Ya ce a lokacin da suka isa wajen, sun iske motar na ci da wuta.

 

Advertisement

 

A cewar Malam Abdul’azizi, bayanai sun nuna motar Hilux din ce ta je ta doki bas din tana tsaka da tafiya, inda nan take ta fadi kuma ta kama da wuta.

Advertisement

 

Sai dai ya ce direba da yaron motar suna Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Shika, inda suke samun kulawa.

Advertisement

 

Duk kokarin jin ta bakin Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Zariya ya ci tura saboda mai magana da yawunsu ya ce ba ya gari bai san yadda lamarin ya faru ba.

Advertisement

 

To sai dai mazauna kauyen sun ce ita motar Hilux din ce take gudun wuce sa’a yayin da take kokarin kwace wa sai direbanta ya hango wata motar da ke zuwa sai ya dawo da baya ya bigi motar fasinja da ke kan hanyar, inda ya kara mata gudu ta kife ta kama da wuta.

Advertisement

 

 

Advertisement

Sun ce mutane sun yi iya kokarinsu wajen cire sauran fasinjoji ciki har suka kone amma suka gaza yin hakan har mutanen suka kone.

 

Advertisement

Hatsarin na ranar Asabar dai daya ne daga cikin da dama da ake yawan samu a wannan hanyar.

 

Advertisement

Ko a baya-bayan nan, wasu motocin tare da wata tankar mai sun yi taho-mu-gama kuma sun kone mutane masu yawa da ransu.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending